Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kulla yarjejeniyar aiki tsakanin BUK da gidan Zoo

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kulla yarjejeniyar inganta dabbobi da jami’ar Bayero a wani mataki na kara fadada ilimin yadda za a kula da dabbobin.

Manajan daraktan kula da gidan Zoo a nan Kano Sadi Kura Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, jim kadan kammala kulla yarjejeniyar a tsakanin su.

Ya ce, yarjejeniyar za ta taimaka wajen samun dabarun inganta dabbobin daji da na gida.

“Muna sane da cewa kowanne gidan adana namun daji makaranta, domin ana zuwa domin a samu ilimi, sai dai mun yanke hukuncin yin hulda da BUK ne domin su taimaka mana wajen yin bincike da samar da sinadaran da za su taimawa wajen bunkasar dabbobin” a cewar Kura Muhammad.

Ya kuma ce, matukar yarjejeniyar ta cimma nasara, al;ummar jihar Kano za su fi kowa amfana da ita.

A nasa bangaren shugaban jami’ar Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas ya ce, jami’ar Bayero za ta amfana ta fannin bincike da nazari na rayuwar dabbobi.

haka kuma, jami’ar za ta samu karin wasu dabbibin da bata da su a baya.

“Wannan yarjejeniya ina mai tabbatar muku za ta samarwa jihar Kano kudin shiga, domin kuwa da zarar mun fara aiwatar da ita dabbobi za su habaka, mutane za su rika zuwa kallo daga ko’ina a fadin kasar nan”. A cewar Farfesa Sagir

Jim kadan bayan kammala kulla yarjejeniyar, hukumomin jami’ar Bayero sun gazaya gidan Zoo din don ganin yadda dabbobin suke rayuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!