Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Zamu samarwa dabbobin da basu da abokan zama abokai: Kano Zoo

Published

on

Kai tsaye: Har yanzu ba’a kama Zakin da ya kubuce ba

 

Hukumar dake Kula da gidan Adana namun Daji ta Zoo dake nan Kano, ta ce za ta samarwa da dabobin dake cikin gidan Abokan zama da hakan zai sa su kara habbaka.

Shugaban hukumar Kwanzabatic Sadik Kura Muhammad ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai dangane da yadda aka gudanar da shagulgulan bikin babbar Sallah a gidan na bana.

Ya Kuma ce hukumar za ta ci gaba da tabbatar da ingancin duk wani Abinci da ake shiga da shi domin sayarwa da Mutane musamman a lokacin bukukuwan Sallah ko Kuma bawa dabbobin dake ciki.

Sadik Kura ya Kuma bukaci Mutane kan su rinka shuka bishiya a gaban gidan su musamman a wannan lokaci na damuna duba da yadda a ko da yaushe ake ci gaba da samun dumamar yanayi.

Ya Kuma nuna takaicinsa kan yadda Mutane ke sare bishiya da zummar yin itace da Ita ko Kuma samar da gawayi.

Ya Kuma bukaci al’umma Kan su ci gaba da baiwa gidan hadin kan da ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!