Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

COVID : 19 – Ganduje ya gana da sarakuna da malamai

Published

on

Biyo bayan sake bullar cutar COVID-19 a sassan duniya a  karo na biyu, jihar Kano ta bayyana cewar mutane goma sha bakwai ne suka rasa rayukan su ta sanadiyar cutar tun daga watan Disambar bara  zuwa Janairu, 2021.

Mataimakin babban jami’i kwamitin Kar ta kwana Kan yaki da Corona Dakta Sabitu Shuaibu Shanono ne ya bayyana hakan a ya yin da Gwamnan Kano ke ganawa da sarakuna guda biyar da hakimai dangane da sake dawowar cutar Karo na biyu.

Dakta Shanono ya ce daga watan Nuwamba 2020 zuwa Janairu, 2021, jihar  Kano ta samu sabbin wadanda suka kamu da cutar har 827 tun bayan da Annobar ta biyu ta zo don haka ya yi kira ga Sarkunan don wayar da kan jama’a kan yadda za su Kare kansu.

A nasa bangaren Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce, gwamnatin ta kirawo sarakunan gargajiya da kuma malamai a jihar saboda su suka fi kusa al’umma adon haka ya ce su wayar da Kan mutane yadda zasu Kare kansu

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta hada kai da jami’an tsaro don tabbatar da cewar ana bin kaidojin cutar.

TWakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan na Kano Kuma shugaban kwamitin COVID-19, Nasiru Yusuf Gawuna.

Ya ce gwamnatin jihar za ta raba abin rufe fuska miliyan 2 a dukkanin masarautu 5 da ke jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!