Connect with us

Labarai

An nada sabon akawun majalisar dokokin Najeriya

Published

on

Hukumar kula da ayyukan majalisun dokokin tarayya ta amince da nadin Mr Ojo Olatunde a matsayin cikakken akawun majalisar dokokin tarayya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Ahmed Amshi.

Sanarwar ta ce, hukumar ta kuma nada Mr. Chinedu Akabueze a matsayin akawun majalisar wakilai.

A ranar goma sha bakwai ga watan Yulin bana ne dai hukumar kula da ayyukan majalisun dokokin tarayyar, ta nada mista ojo da wasu mutane 20 a matsayin shugabanni a majalisun dokokin tarayyar amma na wucin gadi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!