ilimi
An raba kyautar kusan Miliyan 2 ga gwarazan gasar karatun Alƙur’ani na Tiktok

A yau Asabar ne aka kammala gasar Karatun Alkur’ani mai girma ta kafar sadarwar zamani ta Tiktok, wadda fitacciyar ‘yar Siyasa Dakta Maryam Shetty, ta shirya mai taken ‘Recite with Shetty’.
Gasar wadda aka rufe bayan tantance wanda suka shiga da dama daga fadin Najeriya, ta samu halartar Malamai da dama da Hafizai da masu Ruwa da Tsaki a fannin Musabakar Al’kurani mai Girma na Kano.
Da ta ke jawabi yayin karramawar da bada kyauta ga wanda suka samu nasara Dakta Maryam Shetty, ta yi karin haske kan makasudinta na ƙirƙirar gasar.
Inda ta ce, ta yi hakan ne domin janyo ra’ayin mutane da dama wajen gudanar da aikin alheri saɓanin yadda wasu ke yin amfani da kafafen na sada zumunta wajen aikata ba daidai ba.
Haka kuma ta ce, “Na yi farin ciki matuka yadda wannan gasa ta samu dubunnan mutane daga jihohi da dama na Najeriya suka shige ta wanda suna bada gudunmawa sosai inda kowa ya baje hazaƙarsa, wannan babban abun farin ciki ne.”
“Ina kuma miƙa saƙon godiya ta ga dukkan wadanda suka taimaka wajen ganin wannan gasa ta tafi yadda ya kamata, ina ƙara miƙa sako ga matasa da mu dage wajen ci gaba da yin ayyukan alheri a wadannan kafafen,” Inji Maryam Shetty.
A nata ɓangaren ɗaya daga cikin Zakarun gasar Aisha Tahir daga jihar Jigawa da ta zo ta uku, ta bayyana farin cikinta bisa samun nasarar.
Alkalan da suka jagoranci tantance wanda suka lashe gasar sun zabi, Nuraddeen Mu’azu daga birnin Tarayya Abuja , a matsayin na Daya da maki 98, sai Muhammadu Khalid Idris daga jihar Bauchi da maki 97 da digo 7 a matsayin na biyu, sai Aisha Tahir daga jihar Jigawa mai maki 97 da ta zo na Uku.
Wanda ya zo na Daya ya samu kyautar Kudi Naira Miliyan Daya , ya yinda na biyu ya samu Naira Dubu Dari Biyar , kana ta Uku wacce ta samu Naira Dubu Dari Biyu da Hamsin.
You must be logged in to post a comment Login