Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano tayi ta daya a gasar Alkur’ani ta kasa

Published

on

Yar jihar Kano Diya’atu Sani Abdulkadir ce ta lashe mataki na farko a ajin maza da na mata a gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 34 da ya gudana a jihar Legas.

Sai kuma Umar Kabir shima da yayi nasara a mataki na daya daga jihar Kaduna.

Gasar wacce gidauniyar Musabaqa ta jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto ta shirya da hadin gwiwar al’ummar  musulmin jihar Legas mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ne ya bude ta.

Wadanda suka yi nasara sun samu kyautar manyan motoci kirar Nissan Almera da kuma sauran kyaututtuka na kudade.

Motocin da aka bawa wadanda suka yi nasarar a gasar karatun karo na 34 sun hada da wadanda suke mataki na shida na haddar izu sittin na Alkur’ani a Tajwidi da Tafsiri.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!