Labarai
An rantsar da shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal
An rantsar da zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, a matsayin shugaban kasar na biyar, yayin wani katafaren biki a babban birnin kasar Dakar.
Shugabannin kasashen duniya da dama ne suka halarci bikin rantsarwar da suka hada da shugaban Najeriya kuma jagoran kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, Ecowas, Bola Ahmed Tinubu.
Faye ya yi nasara da kaso 54 cikin dari na kuri’un da aka kada a zaben da aka jinkirta a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam’iyyu masu mulki.
A ranar Juma’a ne Kotun Kolin kasar ta yammacin Afirka, ta tabbatar da Faye a matsayin wanda ya ci zaben na ranar 24 ga watan Maris 2024.
Kafin a kai ga zaben, kasar ta yi fama da tarzoma daban-daban bayan da Shugaba Sall ya yi yunkurin jinkirta zaben.
You must be logged in to post a comment Login