Labaran Kano
An rantsar da ”yan majalisar dokoki a Kano
Daga Abdullahi Isa
Majalisar dokokin jihar Kano ta rantsar da sababbin ‘yan majalisar dokokin jihar guda hudu wadanda suka lashe zabukan cike gurbi a baya-bayan nan.
Daraktan kula da harkokin sharia na majalisar, Ahmed Zaharaddin ne ya rantsar da ‘yan majalisun guda hudu da safiyar yau Talata.
Mambobin majalisar da aka rantsar sun hada da: Muhammed Uba Gurjiya daga yankin karamar hukumar Bunkure da Tasiu Ibrahim Zabainawa mai waklitar karamar hukumar Munjibir
Majalisar Kano ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan Goma Sha Biyar
Majalisar ta bukaci gwamnati ta gina makarantun firamare a karamar hukumar Ungogo
sauran sune Kabiru Yusuf Ismail Chinkoso wakilin karamar hukumar Madobi da Kuma Magaji Dahiru Zarewa sabon wakili daga karamar hukumar Rogo.