Connect with us

Labarai

An rufe kasuwar Jilli tun shekaru 5 baya- Gwamna Zulum

Published

on

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce kasuwar Jilli da ke karamar hukumar Gubio, da  aka kai harin sama da ya yi sanadin mutuwar fararen hula, an rufe ta tun shekaru biyar da suka gabata.

 

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Malam Dauda Iliya ya fitar, ya ce gwamnan ya bayyana cewa kasuwar ta zama wurin da ake zargin masu aikata laifuka da masu taimaka musu ke amfani da ita.

 

Gwamnan ya ce ya samu cikakken bayani kan harin saman da rundunar Operation Hadin Kai ta kai a yankin, wanda ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe.

 

Zulum ya kara da cewa gwamnatin Borno na tuntubar gwamnatin Jihar Yobe da manyan hafsoshin soji domin fahimtar abin da ya faru tare  da daukar mataki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!