Labarai
An rufe wuraren taron bukukuwa a jihar Kano sakamakon fara Azumi

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta ba da umarnin rufe dukkan wuraren nishaɗi a jihar nan take, ciki har da gidajen gala da na casu da na tarukan biki.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Talata, umarnin zai fara aiki daga ƙarfe 10:00 na dare a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, kuma zai ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen watan Ramadan mai alfarma.
Hukumar ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne don bai wa mazauna jihar damar yin azumin Ramadan cikin salama da kuma gabatar da ayyukan addini cikin yanayi na natsuwa da kwanciyar hankali.
You must be logged in to post a comment Login