Labaran Wasanni
An sace kofin Afrika da kasar Masar ta dauka
An sace kofin Afrika da kasar Masar ta dauka sau uku a jere a Shalkwatar hukumar da ke Alkahira babban birnin kasar ta Masar.
Hukumar kwallon kafar kasar ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce kofin da a ka dauka ya na daya daga cikin kofunan da kasar ta dauka sau uku a jere.
Tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar ta kasar Masar Ahmed Shobeir ne ya tabbatar da batan kofin.
Ya ce, batan kofin ya biyo bayan gyaran da hukumar ta ke yi na wuraren ajiyar kayan tarihi na kasar.
An bai wa kasar ta masar kofin ne a shekarar 2010, lokacin da ta lashe kofin karo uku a jere wato shekarar 2006 da 2008 sai kuma shekarar ta 2010 inda a ka mallaka mata kofin.
A shekarar 2002 ne a ka fara bai wa kasar Kamaru kofin a karo na farko bayan ta lashe sau uku a jere.
Ahmad Shobeir ya kuma ce, hukumar ta fara gudanar da kwararan bincike game da batan kofin domin lalubo wadanda su ka dauke shi.
Bayan an kai hari ga hukumar kwallon kafa ta Masar a 2013, kofuna da dama da kasar ta taba ci an mayar da su wani dakin ajiya an kulle su.
Hukumar kwallon kafar ta kasar Masar ta tabbatar da cewa, bayan sace kofin an lura da cewa babu wasu sarkoki da a ka ciyo a gasa daban-daban da kasar ta halarta.
Masar dai ita ce kasar da tafi kowacce kasa a Afrika yawan cin kofin na Afrika inda ta dauki kofin karo 7 tun daga shekarar 1957.
You must be logged in to post a comment Login