Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sako ‘yar ‘dan majalisar da aka yi garkuwa da ita a Kano

Published

on

Masu garkuwa da mutane sun saki Juwairiyya Murtala ‘yar ‘dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar karamar hukumar Danbatta Murtala Musa Kore da aka sace.

Jaridar intanet ta Kano Focus ta rawaito cewar, Juwairiyya ta dawo gida, garin Kore na karamar hukumar Danbatta da karfe misalin 3:30 na daren Talata.

Nura Yusha’u Kore wanda ‘dan uwa ne a gare ta shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce ta dawo gida cikin koshin lafiya.

A ranar Asabar da ta gabata ne, wasu masu garkuwa da mutane su kayi awon gaba da Juwairiyya mai shekaru 17 a duniya.

Sai dai har zuwa wannan lokaci hukumomin tsaro a Kano ba su ce komai ba game da sace ta dama dawowar ta gida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!