Labaran Kano
An sami rudani kan ajiye aikin da shugaban hukumar tattara haraji na Kano
An sami rudani kan ajiye aikin da shugagaban hukumar tattara haraji na cikin gida ya yi na jihar Alhaji Sani Abdulkadir Dambo bayan da gwamanan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi daga mukamin sa.
A wata sanarwa da mai bawa gwamnan Kano shawara a harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya sakawa hannu ta ce tuni Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti da zai binciki wasu matsaloli na hukumar a zamanin tsohon shugaban Sani Dembo.
Sannan sanarwar tace gwamnati ta bawa Sani Abdulkadir Dembo takardar Tuhuma tun jiya kuma dama an dakatar da shi daga kan mukaminsa.
Yayin da kuma Shugaban hukumar tattara haraji na cikin gida Sani Abdukadir Dambo ya ce ya ajiye aikin ne don radin kan sa da yammacin yau Alhamis.
Wannan na dauke cikin sanarwar da shugaban hukumar ya aikewa ofishin sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji a dazun nan.
Sai sanarwar dai bata fayece dalilan da suka sanya shugaban hukumar ta tattara haraji na cikin gida Sani Dambo ya sanya yayi murabus ba amma kuma ya godewa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya bashi daba wajen bada gudunmawar sa a gwamnatin jihar Kano.
Amma daga bisani a zantarwar sa da Wakilin Freedom Radio ya yi Adamu Suleman Muhammad a dazun ya bayyana cewar shi ne ya ajiye aikin don radin kansa.
You must be logged in to post a comment Login