Coronavirus
An samu cunkoso a kasuwannin Kano
Biyo bayan karewar dokar hana zirga-zirga ta sati daya da gwamnatin jihar Kano ta sanya a wani bangare na hana yaduwar Cutar Covid-19, gwamnati ta dage dokar na awanni 18 domin baiwa al’umma damar yin siyayyar azumi watan Ramadan.
Kan hakan ne Freedom ta zaga wasu daga cikin kasuwanni a cikin birnin Kano da suka hadar da kasuwar Kantin kwari da Singa da Sabon gari, don ganin yadda ake gudanar da hada-hadar kasuwanci.
Sai dai hanyoyin shiga kasuwannin a cike makil suke da ababen hawa ta yadda mutum zai kwashe awanni a cikin gosulo kafin samun shiga cikin kasuwa.
Haka kuma a cikin kasuwannin shaguna sun kasance cike da jama’a wadanda ke kokarin siyan kayayyaki.
Wasu da Tashar ta Freedom ta zanta dasu akan ababen hawa suna layin shiga kasuwar Singa sun bayyana yadda suka tsinci kansu a wannan yanayi na cunkoso, inda wasu suka bayyana cewa sun shafe awanni a cikin wannnan cunkoson.
Da yawa daga cikin al’umma sun yi kira ga gwamnati kan ta kara yawan lokacin da za’a ringa fita don gudanar da siyayya a cewar su kwana daya yayi kadan wanda kuma hakan ne ke haddasa cin koson jama’a akan titina.
You must be logged in to post a comment Login