Labarai
An samu karancin barazanar tsaro yayin zabe a Kano- Kwamred Ibrahim Wayya
Zauren da ya yi aikin sanya ido a zaben shugaban kasar da ya gudana a jihar Kano ya ce, an samu karancin barazanar tsaro a lokacin zabe da ma bayan kammala zaben.
Shugaban zauren Kwamared Ibrahim Wayya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu Nura Bello da safiyar yau, wadda tattaunawar ta mayar da hankali kan yadda kwamitin ya gudanar da ayyukan sa lokacin zabe.
Kwamared Wayya ya kuma ce, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta taka rawa wajen dakile matsalar sayen kuri’a daga masu zabe.
Shugaban zauren sa ido kan harkokin zabe a nan Kano Kwamared Ibrahim Wayya kenan a zantawarsa da Freedom Radio.
Rahoton: Nura Bello.
You must be logged in to post a comment Login