Labarai
An samu raguwar matasa marasa aikin yi a Nijeriya-NBS
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta fitar da rahoton da ke bayyana cewa an samu ragin matasa da ke fama da rashin aikin yi da kashi 4.1 cikin 100 cikin wata ukun farko na wannan shekara.
Alkaluman rashin aikin yi a baya ya kai maki 33.1 cikin 100 a rahotonta na ƙarshe da ta fitar a ƙarshen shekarar data gabata.
Hukumar NBS kafin wannan lokaci ta ce za ta yi amfani da dabarun fasahar zamani wajen tabbatar da haƙiƙanin alƙaluman ma’aikata da kuma marasa aikin yi a faɗin ƙasar.
A lokacin kaddamar da sabon tsarin fasaha a Abuja, NBS ta ce sabbin alkalumanta za su yi gogayya da irin waɗanda ake gani a ƙasashen Turai wajen sahihanci.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu
You must be logged in to post a comment Login