Labarai
An sanya dokar takaita zirga-zirga a wasu yankunan jihar Kwara

Shugaban Karamar Hukumar Kaiama mai fama da matsalar tsaro a Jihar Kwara, Abubakar Danladi, ya sanya dokar hana fita ta dare a dukkanin fadin karamar hukumar sakamakon matsalolin tsaro da suka biyo bayan harin da aka kai ranar 3 ga Fabrairu a kauyukan Woro da Nuku. Sanarwar ta fito ne cikin wata takarda da aka bai wa jaridar Saturday PUNCH.
Sabuwar dokar ta tanadi hana zirga-zirga daga karfe 9:00 na dare zuwa 5:30 na safe a kowace rana, inda aka haramta duk wani motsi na ababen hawa ko ta kafa a wannan lokaci. Danladi ya ce an dauki matakin ne bayan cikakken nazari kan halin tsaro tare da tuntubar jami’an tsaro da shugabannin al’umma, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma dakile kara tabarbarewar doka da oda.
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa dokar ta wucin gadi ce, ba don tauye harkokin yau da kullum ba, sai dai domin bai wa jami’an tsaro damar shawo kan barazanar da ake fuskanta. Matakin ya zo ne bayan rahotannin cewa sama da gawarwaki 176 aka binne a kaburbura na bai daya bayan harin, yayin da jami’an tsaro suka kara kaimi wajen sintiri a yankin da kewaye.
You must be logged in to post a comment Login