Labarai
An sanya dokar takaita zirga-zirgar mutane a Yauri

Majalisar ƙaramar hukumar Yauri a jihar Kebbi, ta sanar da sanya dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 10:00 na dare zuwa 07:00 na safe har tsawon kwanaki uku.
Shugaban ƙaramar hukumar Abubakar Shu’aibu Ƙauran Yauri, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan ganawar da ya yi da hukumomin tsaro a fadar Sarkin Yauri Dakta Zayyanu Muhammad Abdullahi.
Wannan mataki ya biyo bayan barkewar rikici tsakanin matasan Unguwar Tashar Kattai da wasu masu haƙar zinare a garin Yauri, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi da dama.
You must be logged in to post a comment Login