Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

An sanya ranar fara shari’a tsakanin Farfesa Maƙari da Dr. Abdallah Gadonƙaya

Published

on

Babban limamin ƙasa da ke Abuja Farfesa Ibrahim Maƙari ya shigar da ƙarar limamin masallacin juma’a na Usman bn Affan Sheikh Abdalla Gadonkaya, bisa zargin yi masa ƙazafi.

Cikin takardar ƙara mai lamba CV/327/21 da ke ɗauke da kwanan watan 20 ga Agustan da muke ciki, Maƙari ya buƙaci kotun ta sanya Abdallah Gadonƙaya da ya fito fili ya janye kalamansa.

Haka kuma ta buƙaci da ya bayyana a gabanta ranar 6 ga Satumba mai kamawa domin amsa tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Idan za a iya tunawa a watan da ya gabata ne aka jiyo Malam Abdallah Gadon Kaya, na mayar da martani kan wasu kalamai da ya yi iƙirarin Maƙari ne ya yi su.

Wasu daga cikin kalaman na Malam Abdall ah ga Maƙarin sun ce “Farfesa Maƙari maƙiyin sunnar Annabi (s.a.w) ne, haka kuma duk lokacin da malamai suka yi wa’azi sai ya ƙalubalancesu”

Kazalika an jiyo Malam Abdallah na cewa “duk lokacin da wasu miyagu suka yi ɓatanci ga Annabi sai Maƙari ya fito ya karesu”.

Haka kuma ya ce “malamin ya yi shuhura wajen kare maƙiya ma’aiki”.

Sai dai bayyanar wannan jawabi ne kuma Farfesa Maƙarin, ya ce sam ba zai lamunci ɓatancin da aka yi masa ba.

Hasalima an ga wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafan sada zumunta na zamani da ke ƙaryata kalaman Malam Abdallah cikin wani karatu da malam Maƙarin ya wallafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!