Rahotonni
An shekara 20 da fara shari’ar musulunci a Najeriya
Malamai da mabiya addinin musulunci a jihohin Arewacin kasar nan sun dauki tsawon lokaci suna fafutukar ganin an kafa shari’ar musulunci a sassa daban-daban na kasar.
Biyo bayan kiraye-kiraye na mabiya addinin musulunci ya sanya gwamnan jihar Zamfara a wancan lokacin Ahmad Sani Yariman Bakura ya sanar da cewa jihar Zamfara zata fara aiki da tsari irin na shari’ar addinin musulunci a ranar 27 ga watan Octoba na shekarar 1999.
Jihar Zamfara itace jiha ta farko da ta fara kaddamar da shari’ar musuluncin a ranar 27 ga watan Janairu na shekara ta 2000, sai jihar Kano dake biye mata baya inda gwamnan jihar na wancan lokaci Engr. Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da shari’ar a watan 6 na shekara ta 2000.
Jihar Sokoto da kuma jihar Katsina sun biyewa jihar Kano baya inda suma suka kaddamar da tsarin shari’ar musulunci a karshen shekarar ta 2000.
Jihohin Bauchi, Borno, Jigawa, Kebbi da kuma jihar Yobe suma sun bi sahun sauran jihohin da suka kaddamar da shari’ar tun da farko a shekarar 2001.
Su kuwa jihohin Kaduna, Niger da kuma jihar Gombe sun kaddamar da shari’ar musulunci ne a wasu sassa na jihohinsu da musulmai ke da rinjaye, kasancewar suna da al’umma da dama masu mabam-bamta addini a jihar.
Al’ummar musulmi dai sunyi farin ciki matuka da kaddamar da shari’ar a wancan lokaci.