Labarai
An shiga fargaba a Kano bayan ɓullar wasu mutane a kan raƙuma
Al’ummar wasu unguwanni a nan birnin Kano sun shiga fargaba sakamakon ɓullar wasu mutane da ke yawo a kan raƙuma ɗauke da kayayyaki.
Yankunan da aka samu ɓullar waɗannan mutane sun haɗa da Rimin Zakara da ke ƙaramar hukumar Ungogo sai kuma Ɗorayi Babba da ke ƙaramar hukumar Gwale.
Wasu cikin al’ummar unguwannin sun shaida wa Freedom Radio cewa, mutanen na yawo a kan raƙuma ɗauke da ƙunshin kayayyaki da ba a san menene ba.
To sai dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta yi bincike a kansu ta kuma gano cewa basu da wata illa, kasuwanci ne ya kawo su Kano.
DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun ƴan sandan Kano.
Ya ce, binciken su ya gano cewa, mutanen sun zo Kano ne domin kasuwanci inda suke sayar da kanwa su sake siyan kayayyaki su koma Nijar.
Rundunar ƴan sandan ta kuma yi kira ga al’ummar yankunan da su kwantar da hankalin su, domin babu wani abin shakku game da baƙin mutanen.
You must be logged in to post a comment Login