Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda sun kama matasa 49 bisa zargin satar kaya a Triumph

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, ta fara gudanarda bincike a kan wasu matasa 49 da ta cafke  bisa zargin hada kai da satar kayan mutane a shagunan tsohuwar madaba’ar Triumph da ke karamar hukumar Fagge.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

Kiyawa ya ce, rundunar ta kama matasan ne da kayayyakin sata da suka hada da na’urar sanyaya daki guda 4, Kofofi da Tagogi da sauran wasu kayayyaki.

Haruna Kiyawa ya kuma ce, yanzu haka kwamishinan ‘yan sandan Kano Muhammad Hussain Gumel ya bada umarnin ci gaba da binciken matasan domin gurfanar da su a gaban Kotu.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, Kwamishinan ƴan sandan na Kano, ya kuma yi kira ga iyayen yara da kuma masu fada a ji a unguwanni da su rika gargadin matasa wajen kaucewa satar kayan mutane, domin duk wanda suka kama ba zasu kyaleshi ba.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!