Kimiyya
An shiga ruɗani bayan katsewar Facebook, WhatsApp da Instagram

Facebook da WhatsApp da Instagram sun katse, abin da ya shafi miliyoyin masu amfani da shafukan a duniya.
BBC Hausa ta rawaito cewa kafofin sun daina aiki a Washington na Amurka da Paris da London da sauran biranen duniya.
Matsalar ta shafi masu amfani da shafukan a Najeriya.
Daya daga cikin shugabannin Facebook ya faɗa a Twitter cewa suna ƙoƙarin gano matsalar da daidaitawa cikin gaggawa.
You must be logged in to post a comment Login