Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Rahoto: Yadda shara ke barazanar lalacewar titin jirgin ƙasa a Kano

Published

on

Wani al’amari da ake ganin barazana ce ga muhalli shi ne yadda ake zubar da shara akan layin dogo musamman ma idan ya ratsa ta cikin unguwanni.

Tuni dai hukumomi ke gargaɗi kan zubar da bola akan hanyar da jirgin ƙasa  ke wucewa sakamakon hatsarin da zai iya haifarwa.

A cewar masana muhalli ma zubar da shara barkatai barazana ce ga lafiyar al’ummar da ke rayuwa a yankin, kuma zai iya janyo hatsarin jirgin ƙasan idan da tsautsayi.

A zantawar mu da wasu daga mazauna unguwannin da layin dogon ya ratsa irin su Sharada, Gandu da sauran su, sun bayyana cewa..

Malam Shehu Ibrahim da ke zaune a Sharaɗa gidan Maza ya ce “Mazauna unguwar ne suke zubar da shara, amma wani lokacin akwai ƙarancin guraren zubar da sharar shiyasa ake zubarwa ko’ina”.

Shi kuwa Malam Jibrila Ya’u mazaunin unguwar Gandu cewa yayi “A lokacin  baya wasu daga cikin mutanen unguwar suna hanawa ,amma daga baya da suka  gaji  suka daina sabida akwai ƙarancin guraren zubar da shara”.

Malam Umar shi ma ya ce “Muna sane da illar zubar da shara akan titin jirgin ƙasan, amma babu yadda za mu yi ne shiyasa muke zubarwa a duk inda muka samu, kuma hakan zai ƙara janyo hankalin gwamnati ta san matsalar mu”.

Sai dai mazauna unguwannin sun buƙaci gwamnati ta kawo musu babban abin zuba shara ko kuma hukumar kula da titin jirgin ta kawo musu don kiyaye matsalar zubar da sharar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!