Ƙetare
An tilasta wa jirgin sojin saman Najeriya sauka a Burkina Faso- Mahukunta

Gwamnatin Burkina Faso ta ce an tilastawa wani jirgin saman sojin saman Najeriya , da ke ɗauke da sojoji 11 sauka a ƙasar a ranar Litinin bayan da aka ce ya keta sararin samaniyar ƙasar ta.
Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin ƙasar ta ce jirgin sojan na ɗauke da ma’aikata biyu da fasinjoji tara a cikin sa kuma dukkansu jami’an soji ne, da binciken da hukumomin ƙasar Burkina Faso suka gudanar ya nuna cewa jirgin ba shi da izinin shawagi a sararin samaniyar ƙasar.
Ƙungiyar AES ta yi alla-wadai da lamarin tare da kakkausan suka kan keta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke cikin ƙungiyarta.
Haka kuma Ƙungiyar, ta yi gargaɗin ɗaukar mataki kan duk wani jirgi da ya keta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke yankin da tare da izini ba.
You must be logged in to post a comment Login