Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda sun nemi Buhari ya samar da kotun hukunta masu fyade

Published

on

Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da wata kotu ta musamman da zata rika sauraren kararrakin Fyade don yanke hukunci cikin sauri.

Mataimakin sufeton janar na ‘yan sandan kasar nan mai kula da sashen binciken Sirri Ibrahim Lamurde ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke karbar bakuncin shugaban hukumar kare hakkin Dan Adam Tony Ojukwu da yannacin jiya Juma’a a birnin tarayya Abuja.

Ibrahim Lamurde ya ce samar da irin wadannan kotuna zai taka rawa wajen takaita ayyukan Fyade da ake yawan samu a kasar nan da kuma kwatowa wadanda aka yiwa hakkin su baya ga hukunta masu aikata wannan mummunar dabi’a.

A yayin na sa jawabin shugaban kumar kare hakkin Dan Adam na kasa Tony Ojukwu ya ce dama kwato hakkin Dan Adam shine aikin hukumar, kuma hukumar zata bada dukannin gudunmowar da ta dace don ganin hakan ta tabbata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!