Labaran Kano
An ware naira biliyan uku domin gina ajujuwa a jahar Kano.
Shugaban kwamitin ilimi a majalisar dokokin jahar Kano Muhammad Bello Butu-butu kuma wakilin ilimi na kananan hukumomin Rimin gado da Tofa a zauren Majalisa ya bayyana cewa dokar bada ilimi kyauta a Jihar nan, ya shafi kudaden da dalibai suke biya gaba daya tun daga kan makarantun firamare, har sakandire.
Muhammad Bello Butu-Butu ya bayyana hakan ne a yau jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Radio Freedom.
Ya ce jarrabawar kwalifayin da yake da a mataki uku, yanzu ya koma biyu, wanda yaci ya wuce, Wanda ya fadi ya maimaita.
Yace duk makarantar da aka kama da laifin bawa dalibai ansa yayin jarrabawa, ko kuma cin hanci da rashawa, shakka babu za’a hukuntasu dai-dai da laifinsa.
Yace idan har aka sabunta asusun tallafawa ilimi da ake sa ran kafawa, suna sa ran nan da shekara guda ma makarantun gwamnati za su sha gaban ta kudi.