Labarai
An yaba wa karin da aka yiwa dillalan fetur -Hafizu Kawu
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tarauni kuma shugaban kwamitin dake kula da bankuna da harkokin kudi na majaisar wakilai Alhaji Hafizu Ibirahim ya bayyana cewa karin kudin da aka yiwa dillalan man fetur na taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Alhaji Hafizu Ibrahim Kawu ya bayyana hakan ne a yau, jim kadan bayan kammala shirin barka da hansti na nan Freedomn radiyo wanda ya mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi man fetur da batun rufe iyakokin kasar nan.
Sai dai Hafizu Kawu ya ce karin kudaden da aka yiwa dilalan man fetur bai shafi kananan ‘yan kasuwa ba a dn haka karin ba zai kasance ata takura ga jama’a ba.
Majalisar wakilai za ta kaddamar da shugabannin kwamitoci
Majalisar wakilai zata binciki manyan ayyukan gwamnatin tarayya tun daga 1999
Majalisar wakilai ta yi barazanar kin bayyana a taron gabatar da kasafin badi
Ya ce wannan karin da aka yi ya kuma taka rawa wajen rage yawan rancen da kasar nan ke ciyo wa don cike wani gibi na kasafin kudi,ya na mai cewa idan aka dore a haka to kuwa shakka babu za’a daina karbo bashi kwata-kwata.
Daga nan kuma sai kawu ya bukaci a’ummar Najeriya dasu rika baiwa gwamnati hadin kai a duk lokacin da ta bijiro da wani sabon tsari a cewar sa gwamnati ba zata samar da tsare-tsaren da zasu cutar da jama’a kasar nan ba.