Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar wakilai za ta kaddamar da shugabannin kwamitoci

Published

on

Majalisar wakilai ta sanar da cewa a ranar 2 ga watan Oktoba mai zuwa ne za ta kaddamar da shugabannin kwamitocinta da mataimakansu.

Mataimakin shugaban Majalisar Ahmad Wase ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na yau, inda ya ce nan gaba kadan za su fitar da sunayen mambobin kwamitocin.

Ya kuma kara da cewa nan ba da jimawa ba za su gana da shugabannin kwamitocin da mataimakansu, don fidda tsare-tsaren yadda ayyukansu za su kasance.

A ranar 25 ga watan Yulin da yagabata ne dai shugaban majalisar ta wakilai Femi Gbajabiamila ya sanar da sunayen shugabannin kwamitocin da kuma mataimakansu.

Haka zalika majalisar ta bukaci duk kwamitocin wucin gadin da majalisar ta kafa su gaggauta mika rahotanninsu nan da makonni biyu masu zuwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!