Labarai
An yi garkuwa da alkalin
Da safiyar yau Laraba ne masu garkuwa da mutane suka sa ce alkalin babbar kotun tarayya justice Dogo akan hanyar sa ta zuwa Akure daga babban birinin tarayya Abuja.
Rahotanni sunyi nuni da cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa na naira miliyan 5 kafin su sake shi.
Tuni dai babban sefton yan sandan kasar nan ya umarci shugban sashin kula da bincike na musamman Abba Kyyari da ya bazama zuwa Akure domin kubutar da jojin.