Labarai
An yi hasashen mummunar ambaliyar ruwa a Kano da wasu jihohi 27 a daminar bana- Minista

Gwamnatin tarayya ta yi hasashen cewa akwai alamun samun ambaliyar ruwa a daminar bana a wasu jihohin kasar nan 28 ciki har da nan Kano.
Ministan albarkatun ruwa Suleiman Adamu ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.
Ya ce lamarin zai faru ne a kananan hukumomi 121 da ke jihohi 28
Sai dai ya ce jihohin da ake tsammanin lamarin zai fi muni sun hada da: Lagos, Cross River, Rivers, Bayelsa Delta da kuma Ondo.
You must be logged in to post a comment Login