Labaran Kano
An yi shagalin bikin sunan Akuya a Kano
An shiryawa wata Akuya mai suna Abida mai shekara daya a duniya kasaitaccen bikin suna don taya ta murnar haihuwar da Namiji a jihar Kano.
Mai Akuyar mai suna Rukayya Muhammad Lawal ‘yar Asalin jihar Zamfara dake zaune a Kano , tace dalilin da yasa ta shiryawa Akuyar tata bikin sunan a yau, ta shafe sama da shekaru Ashirin dayin Aure kuma ta haifi ‘ya’ya bakwai amma duk sun mutu babu wanda yayi saura hakan yasa ta sayi Akuya da ta yiwa lakabi da suna Abida, kuma Allah ya albarkace ta da haihuwar da Namiji ta Kuma saka masa suna Murtala a yayin bikin sunan da aka yi a yau.
Rukayya Muhammad Lawal ta kara da cewa haihuwar da Akuyar tata tayi, ya sanya ta matukar farin ciki wanda hakan yasa ta shirya gagarumin suna ta kuma gayyaci mutane daga wurare daban-daban don su zo su tayata farin ciki , sun kuma yi girke-girke kala daban-daban domin nuna farin ciki da haihuwar Akuyar Abida.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya halarci taron bikin sunan ya ruwaito cewa a yayin taron sunan an yiwa Akuyar Abida kasaitacciyar kwalliya ta gani ta fada tare dan Akuyan data haifa mai suna Murtala.
Ku kalli bidiyon tattaunawar Freedom Radio da mai akuyar.
RUBUTU MASU ALAKA:
An yi shagalin bikin sunan Akuya a Kano
Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa