Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An yi shagalin bikin sunan Akuya a Kano

Published

on

An shiryawa wata Akuya mai suna Abida mai shekara daya a duniya kasaitaccen bikin suna don taya ta murnar haihuwar da Namiji a jihar Kano.

Mai Akuyar mai suna Rukayya Muhammad Lawal ‘yar Asalin jihar Zamfara dake zaune a Kano , tace dalilin da yasa ta shiryawa Akuyar tata bikin sunan a yau, ta shafe sama da shekaru Ashirin dayin Aure kuma ta haifi ‘ya’ya bakwai amma duk sun mutu babu wanda yayi saura  hakan yasa ta sayi Akuya da ta yiwa lakabi da suna Abida,  kuma Allah ya albarkace ta da haihuwar da Namiji ta Kuma saka masa suna Murtala a yayin bikin sunan da aka yi a yau.

Rukayya Muhammad Lawal ta kara da cewa haihuwar da Akuyar tata tayi, ya sanya ta matukar farin ciki wanda hakan yasa ta shirya gagarumin suna ta kuma gayyaci mutane daga wurare daban-daban don su zo su tayata farin ciki , sun kuma yi girke-girke kala daban-daban domin nuna farin ciki da haihuwar Akuyar Abida.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya halarci taron bikin sunan ya ruwaito cewa a yayin taron  sunan an yiwa Akuyar Abida kasaitacciyar kwalliya ta gani ta fada tare dan Akuyan data haifa mai suna Murtala.

Ku kalli bidiyon tattaunawar Freedom Radio da mai akuyar.

RUBUTU MASU ALAKA:

An yi shagalin bikin sunan Akuya a Kano

An fara gyaran gadar Zawaciki

Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!