Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

An yi wa kwamitin ciyar da ɗaliban Kano garambawul

Published

on

Gwamnatin tarayya ta yiwa kwamitin kula da harkokin ciyarwar ɗalibai a jihar Kano garambawul.

Ta yadda a yanzu zai bada dama wajen sanya idanu sosai a ɓangaren ciyar da ɗalibai abinci a makarantun jihar Kano.

Ministan jin ƙai da kare abkuwar ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan shirin ciyarwar ɗaliban  kano tare da ƙaddamar da kwamitin da zai kula d harkokin ciyarwar.

Ministar wadda ta samu wakilcin mataimakinta na musamman Abubakar Ibrahim Hashim ya ce “mun samu rahoton yadda ake tafiyar da harkokin ciyar da ɗalibai abinci a makarantun firamare na gwamnati a Kano, wannan ne ya sanya muka zo domin yin garambawul ga shirin kuma muna buƙatar sanya tsoron Allah a lamarin domin kuwa dukkanin waɗanda ake ciyarwar yaran mu ne”.

“Idan yaran mu sun samu abinci mai kyau ilimin su zai bunkasa kuma za su samu kyakyawar rayuwa” a Cewar ministan.

An ƙaddamar da kwamitin da zai riƙa kula da harkokin ciyar da ɗaliban Firamare na jihar Kano abinci, domin inganta harkokin koyo da koyarwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!