Labarai
An yi jana’idar mutagen da ‘yan bindi suka kashe a Katsina
Da karfe 11 na safiyar wannan rana ta Laraba ne aka yi jama’izar mutane 18 da ‘yan bindiga suka halaka a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina bayan da aka yi musu sallah a fadar sarkin Katsina.
Babban limamin Katsina, Alhaji Mustapha Ahmed ne ya jagoranci sallar da aka yiwa wadanda ‘yan ta’addan suka kashe a daren jiya Talata.
Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman tare da ‘yan majalisarsa da fadawa da sauran jama’ar jihar ne suka halarci jana’izar mamatan.
Bayan kammala jana’azar ne Sarkin Ruma kuma hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, ya bayyabawa manema labarai cewa yanzu haka jami’an ‘yansanda na aiki tukuru don bankado wadanda suka aikata kisan.
Haka kuma ya yi kira ga shugaban kasa, Muhammad Buhari da ya karbe ikon tsaron yankin daga hannun ‘yansanda zuwa sojoji da nufin shawo kan matsalar tsaron yankin da gaggawa.
Ya ce lamarin na bukatar a magance shi da gaggawa don hana mutane daukar doka a hannu.