Connect with us

Labarai

 An zargi DPO da hannu wajen kisan kai

Published

on

Lauyoyin Kare hakin dan Adam na cigaba da Bincike akan matashin nan da “yan sandan madobi suka doka har ta kai ga  ya dukan yayi sanadiyyar  mutuwar sa.

An gano cewa baturen ‘’yansanda na Madobi  na da hannu wajen dukan  matashin  inda a wani bangare “yan sandan masu bincike sun ce  basu kama baturen yansandan da  laifin da ake zargin sa dashi ba .

Lauya dan gwagwarmaya  Barrister  Abba Hikima Fagge, yace zasu cigaba da bibiya domin gane gaskiyar al’amarin da yadda bincike yake tafiya, sannan kuma  ya kalubalanci hukumar “yan sanda akan kyale  baturen ‘’yansandan da ake zargi da  cigaba da harkokin sa ba tare da an tsare shi ba duk da zargin  da ake masa da  sak hannu wajen dukan wannan bawan Allah da takai  har ya rasu.

A nata bangarin rundunar  “yan sandan Jihar Kano  ta hanyar mai magana da yawunta, D.S.P Abdul Haruna Kiyawa yace har izuwa yanzu binciken su bai nuna  cewa wannan baturen ‘’yansanda na Madobi  na da hannu a dukan  wannan bawan Allah amman suna cigaba da bincike kuma zasu yi Adalci.

Yadda matashi ya rasa ransa a hannun ‘yan sanda

‘Yan sanda sun cafke sojoji kan KAROTA

Zamu dauki mummunan mataki kan Zakin da ya kubuce –‘Yan sanda

A wani labarin kuma “yansandan  Shiyya ta daya dake Kano sun kama wasu “yan sanda da suke amfani da kayan kaki suke karbar kudi a hannun mutane a Unuguwar Sabon Gari .

Kakakin rundunar S.P Sambo Sokoto yace suna cigaba da bincike akan wadannan mutane da aka kama kuma iya binciken da sukayi  ya tabbatar da cewa babu wani Dansanda a cikin wadannan mutanen.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,797 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!