Ƙetare
Ana ci gaba da kokarin zakulo mutanen da suka makale bisa ruftawar Mahakar ma’adanai a Ghana

Hukumomi a kudancin kasar Ghana, sun ci gaba da aikin ceto wasu masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da ake fargabar sun makale a ƙarƙashin wata mahaƙa da ta rufta a Larabar makon nan.
An tabbatar da mutuwar mutum uku, yayin da wani mutum guda ke kwance a asibitin cikin mawuyacin hali, bayan ruftawar mahaƙar da ke ƙauyen Akyem Wenchi a gundumar Denkyembour a yankin gabas.
Jamai’a na cewa ana fargabar cewa akwai mutum 30 da suka maƙale bayan rufawar mahaƙar.
Kawo yanzu ba a san dalilin da ya haifar da ruftawar mahaƙar ba.
Jami’an tsaro sun fice daga yankin, bayan da wasu fusatattun matasa da mazauna yankin suka mamaye mahaƙar a lokacin da ake aikin ceton.
You must be logged in to post a comment Login