Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ana cigaba da dambarwa tsakanin ‘yan farm center da KAROTA

Published

on

Bayan da aka yi bikin ranar tabbatar da adalci ta duniya a yau, ‘yan kasuwa waya ta Farm Center dake nan Kano, na kokawa kan rashin adalci da suke zargin wasu mahukunta na kokarin yi musu.

Da fari dai ‘yan kasuwar sun garzayo tashar Freedom Rediyo hannunsu a ka, kan wani abin alhini da suka ce barazana ce ga rayuwarsu wanda kuma ka iya jawo rashin tsaro a jihar nan.

‘Yan kasuwar suka ce haka-sakit suka samu wata wasika wacce kalaman cikin ta, tamkar kalaman tayar da husuma ne, wadanda idan har za’a yi li’irabin su dalla-dalla, to fa tamkar kokarin zunguro sama ne da kara, ko kuma dai kalmar yan hausa ke cewar fitina na bacci amma an tayar da ita.

Sai dai wannan dai ra’ayoyin su ne, to amma shugabancin kasuwar yayi bayanin cewar hukumar KAROTA ce ta aiko musu da wata wasika wacce acikin take umarnin su kan su tattara dukkan kayayyakin su bar kasuwar.

Kunshin wannan wasika wacce sakataren hukumar KAROTA Mutawakkilu Ishak Muhammad ya sanyawa hannu a madadin shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi, ta bukaci duk wani dake da shago ko kwantaina ko kuma tebur da ya hanzarta tashi daga kasuwar, domin kuwa an rufe wannan kasuwar gaba kidayan ta, za’a koma kasuwar Kanawa dake can Dangwauro.

Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA

Da sahalewar ‘yan kasuwar waya ta farm Center- KAROTA

Kano: Hukumar KAROTA ta kai sumame wajen boye magunguna

Sai dai kuma ‘yan kasuwar ta Farm Center sun bayyana matukar takaici da fargaba akan wannan notice, Bala Nuhu Shetima guda ne daga cikin yan kasuwar yace ba zasu taba yin biyayya ga wannan umarni ba domin babu ruwan KAROTA da kasuwa tun da dai kasuwa ai ba mota bace.

Kwamaret Sa’idu Ibrahim Nakowa shine sakataren kungiyar kasuwar yace an dade ana muzgunawa kasuwancinsu, kuma ko kadan wannan umarni ba zai samu gindin zama ba.

To amma anata bangaren hukumar KAROTA tace duk matakin da zata dauka takan dauka ne da kyakyawar niyya domin magance wata barazana da hukuma ta gano, shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ya ce akwai tarin matsalolin da suka hango wanda ka iya zama barazana anan gaba matukar an bar wannan kasuwa tana ci ba.

Baffa Babba Danagundi shugaban hukumar KAROTA na jihar Kano y ace akwai tarin matsaloli da idan aka bar Kasuwar tana ci ba tare da daukar mataki ba.

Sai dai masana shari’a irinsu Barista Abba Hikima na ganin cewa, hukumar KAROTA  bata da hurimi kan daukar matakin kuma dokar da ta kafa hukumar ta sahale musu ne kawai wajen duba zirga-zirgar ababan hawa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!