Coronavirus
Ana gab da kammala jigilar ƴan kasar nan dake ƙasashen ƙetare – Boss
Gwamnatin tarayya ta ce za ta kammala jigilar dawo da yan kasar nan da suka makale a kasashen ketare a ranar Asabar mai zuwa 22 ga watan Agustan da muke ciki sakamakon annobar corona.
Shugaban kwamitin yaki da cutar corona na gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan, lokacin da yake bayar da rahoton cutar ga kwamitin a birnin tarayya Abuja.
Boss Mustapha wanda kuma shi ne sakataren gwamnatin tarayya, ya ce ganin cewa a yanzu ana dab da kammala jigilar yan kasar nan da suka rage a kasashen waje, ya sanya gwamnatin tarayya ta amince da sauran filayen jiragen kasar nan su fara shirin ci gaba da ayyukan su.
Kazalika Boss Mustapha ya ce, a kwai kasashe irin su Amurka da hadaddiyar daular larabawa wato Dubai da kuma Masar wadanda suka shirya domin dawo da yan asalin kasar nan da suka aikata laifuka a can kuma suka yafe musu.
Da yake nasa jawabin ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire ya ce, a yanzu haka ana samun raguwar masu kamuwa da cutar corona a kwanakin nan, yana mai cewa hakan ba zai sanya su rage daukan matakan kariya daga cutar ba.
Dakta Osagie ya kara da cewa a yanzu gwamnatin tarayya ta mayar da hankali ne kan yadda za a rage yawan masu mutuwa sandiyyar cutar a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login