Connect with us

Coronavirus

Corona: An haramta wa matafiya daga kasashen Brazil, Indiya, Turkiya shigowa Najeriya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta haramtawa matafiya daga kasashen India da Brazil da kuma Turkiyya shigowa Najeriya sakamakon tsananin da annobar cutar Corona ta yi a kasashen.

Shugaban kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban kasa kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau.

Boss Mustapha ya ce matakin zai fara aiki ne a ranar talata mai zuwa, sannan kuma za a sake nazartar batun bayan makonni hudu.

To sai dai ya ce ‘yan Najeriya mazauna wadannan kasashe da ke son shigowa kasar za a killace su har tsawon kwanaki bakwai domin tantance lafiyarsu kafin barin su su shigo cikin kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!