Labarai
Ana gudanar da zanga-zangar neman inganta rayuwar yan sanda a Abuja

Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman inganta rayuwar yan sandan Najeriya a birnin tarayya Abuja.
Dan gwagwarmayar nan kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Omoyele Sowore, ne ya jagoranci gungun masu zanga-zangar.
Masu gudanar da wannan zanga-zanga, sun bukaci gwamnati ta duba halin kuncin da ‘yan sanda ke fuskanta, musamman yadda albashinsu ke ƙasa da kima, tare da rashin kula da ‘yan sanda da suka yi ritaya.
Haka kuma, sun ce, lokaci ya yi da za a mutunta waɗanda ke bayar da rayukansu don kare lafiyar jama’a da dukiyarsu.
Sowore ya bayyana cewa, “Yan sanda su ne ginshiƙin tsaro a ƙasa, amma ana wulaƙanta su da iyalansu.
Ya kuma ce ba za su ci gaba da shiru ba alhali suna rayuwa cikin talauci bayan shekaru da dama na hidima.
Masu zanga-zangar sun rike kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce kamar:
“A biyan ‘yan sanda albashi mai kyau yanzu!”
“Rayuwa mai kyau ga masu ritaya!”
“’Yan sanda ma mutane ne!”
Zanga-zangar na gudana ne cikin lumana, tare da jami’an tsaro da suka tabbatar da zaman lafiya a wajen.
You must be logged in to post a comment Login