Labaran Kano
Ana kama mutane idan sun yi dare a Kano
Mutane a jihar Kano na cigaba da kokawa kan yadda jami’an ‘yan sand ke kama su bisa cewa sun yin dare har ma su garkame su, tun daga dare har zuwa safiya a ofishinsu ya yin daga bisani suke yi musu barazanar bada su beli ko kuma su aikewa da su kotu.
A cewar mutane , a wasu lokutan ma akan gurfanar da irin wadannan mutane ba tare da an basu damar sanar da ‘yan uwansu ba.
Mutanen dai na kuma yin korafin cewa, a wasu lokutan ba a basu damar kare kansu kasancewar, ba a kama su da wani laifi ko kuma kayan laifi ba sai dai idan gari ya waye ne za a bukace su da su bada kudin beli gabanin a sake su.
Wani magidanci da ya nemi a sakaya sunan sa mai sana’ar hakar Rijiya wanda ke daya daga cikin mutanen da ‘yan sandan ofishin Sheka suka kama shi lokacin da yake komawa gida a hanyarsa ta dawowa daga daukar karatun alkur’ani mai girma ya shaida wa Freedom Radio yadda ‘yan sandan suka tsare shi har ya kwana ba tare da iyalansa sun san halin da yake ciki ba.
Haka kuma magidancin ya shaida yadda ‘yan sandan suka sanya shi ya bada jinginar wayarsa ta hannu domin a ranta masa kudin beli gabanin su sake shi.
Barista Rukayya Ibrahim Musa, lauya ce a nan Kano ta ce babu wata doka da ta baiwa jami’an ‘yan sanda damar kama mutum da sunan ya yi dare, sai dai har idan an kama shi da kayan laifi ko kuma ya aikata wani laifi.
Sai dai ko da Freedom Radio ta tuntubi mai Magana da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, har yanzu beli kyauta ne a ofisoshin ‘yan sanda.
Wakilinmu Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bukaci duk wanda aka yiwa irin wannan cin zarafi da ya hada kai da ‘yan kwamitin ‘yan sandan da jama’a don hukunta dan sandan da ya aikata laifin.
You must be logged in to post a comment Login