Labarai
Ana samun kasuwannin dabbobi barkatai a Kano – Kungiya
Hadaddiyar Kungiyar masu sana’ar sayar da dabbobi ta jihar kano ta bukaci gwamnatin da ta yi duba kan yadda ake samun kasuwannin sayar da dabbobin ba bisa ka’ida ba.
Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Sule Dan Tsoho ne ya bayyana haka ta cikin shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan tashar Freedom Radio wanda ya mayar da hankali kan abubuwan da suke gudana a kasuwar dabbobi duba da karatowar sallah layya.
Ya kuma ce yawaitar wuraran yana haifar musu da matsaloli tare da gubata harkar sana’ar tasu.
Shugaban ya kuma bayyana cewar a bana an sami karancin hada-hadar a kasuwanin sayar da dabbobin, inda ya alakanta haka da rashin kudi a hannun jama’a sakamakon halin da annobar corona ta sanya tattalin arzikin kasar nan.
Bashir Sule Dan tsoho ya kuma ce tsadar dabbobi a bana ya ta’allaka ne da rashin samun damar fitar da dabobin zuwa wasu jihohin kasar nan da kuma yadda aka kashe kudi wajen kiwata su.
You must be logged in to post a comment Login