Connect with us

Kaduna

El-rufa’i ya bada umarnin tashin masu sayar da dabbobin layya a bakin titi

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bai wa masu sayar da dabbobi a bakin titunan jihar wa’adin awanni 24 kan su tashi daga wuraren da suke sana’ar.

Hakan na kunshe ne, cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Isma’il Dikko shugaban hukumar tsara birane ta jihar Kaduna wato KSUPDA wadda aka rabawa masu sana’ar sayar da dabbobin layya a ranar Talata.

Bisa al’ada dai a duk lokaci irin wannan da babbar sallah ke karatowa akan samu sabbin kasuwannin dabbobi na wucin gadi a wasu wurare dake kusa da al’umma sabanin kasuwanni awaki dake zama na din-din.

To sai ku biyo mu a shirin mu na rana domin jin martanin masu sana’ar sayar da dabbobin, da ma fashin bakin masana kan wannan batu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!