Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana samun rarar biliyan 4 a kullum bayan aiwatar da IPPIS – Akanta

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce ta samu rarar naira biliyan ashirin da daya daga ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnati bayan kaddamar da tsarin biyan albashi na IPPIS.

Haka zalika ta ce gwamnati na samun rarar naira biliyan hudu a kullum sakamakon kaddamar da tsarin na IPPIS a ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnati guda dari shida da biyu.

Akanta janar na tarayya Ahmed Idris ne ya bayyana hakan lokacin da yak e ganawa da ‘yan kwamitin kula da sadarwa na majalisar dattijai wadanda suka kai masa ziyara ofishinsa da ke Abuja.

Haka zalika akanta janar na tarayyar ya kuma ce ofishinsa na yin hadin gwiwa da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro don dakile fitar da bayanan sirri na gwamnati don gudun fadawarsu hannun batagari.

Da ya ke mai da jawabi shugaban kwamitin kula da sadarwa na majalisar dattawa Sanata yakubu Oseni, y ace kasar nan na fuskanta matsaloli da dama da suka shafi kutse da batagari ke yi ga bayanan sirri na gwamnati ta internet

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!