Labarai
Ana wata-ga-wata: Buhari ya kara farashin man fetur zuwa 212
Hukumar kayyade farashin man fetur ta kasa (PPPRA) ta kara farashin man fetur zuwa naira dari biyu da goma sha biyu da kobo shida.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta PPPRA ta fitar a daren jiya, ta ce yanzu litar man za a rika sayar da ita ne akan naira dari biyu da goma sha biyu.
Sanarwar ta ce a yanzu tataccen man fetur yana isowa kasar nan ne akan naira dari da tamanin da tara da kobo sittin da daya, yayin da farashin dapo-dapo ake sayarwa akan naira dari biyu da shida da kobo arba’in da biyu.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan sanarwar da kamfanin mai na kasa NNPC ya yi, wanda ya ba da tabbacin cewa ba za ayi karin farashin mai a watan Maris ba.
You must be logged in to post a comment Login