Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

‘Yan bindiga sun sace ‘Dalibai a jihar Kaduna

Published

on

‘Yan bindiga sun sace dalibai ashirin (20) a kwalejin nazarin kimiyyar daji ta kasa da ke Mando a jihar Kaduna.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan da wasu ‘yan bindigar suka sace mutane goma sha biyu a rukunin gidajen ma’aikatan hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa da ke Kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun sace daliban ne da misalin karfe daya na dare.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, an yi musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da sojoji wanda sanadiyar hakan sojoji suka ceto wasu daliban dari da hamsin da shida wadanda ‘yan bindigar su ka yi yunkurin sace su.

Haka zalika kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da gidan radio BBC Hausa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!