Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ana zargin hukumar kasuwar Kantin Kwari da zama saniyar tatsa – Anti Kwarrafshan

Published

on

A makon jiya dai, hukumar Anti corruption karkashin Barr Muhiyi Magaji Rimingado ta fitar da sanarwar dakatar da duk wata kankanba ta karbewa mutane kudi balle ma akai ga maganar kama yan china a kaisu ofis a tilasta musu biyan naira miliyan guda.

Wannan matsala dai ta kai intaha inda yan kasuwar ke cewar shikenan an tasamma kawo karshen martabar kasuwar.

Sai dai kuma shigar hukumar Anti-corruption ya faranta zuciyar yan kasuwa musamman ma inda ta haramta karbar ko sisin kobo daga hannun kowa,
Wani tuntube dadin gushi kuma shine dakarun hukumar ta Anti-corruption sun kai sumame kasuwar sun kuma cafke wasu kusoshin ofishin manajan darekta su 3,aka kuma yi awon gaba dasu zuwa ofishin hukumar.

Amma dai kuma wata majiya daga hukumar ta Anti-corruption ta shaidawa in da ranka cewar a wannan kokari da suke na yin amfani da sashi na 15,na dokar su da ya basu damar hana zalunci,sai gashi wani babban kusa yana kokarin yin amfani da ikon sa wajen hana hukumar hana wnanan cin zali.

Majiyar tace, wannan babban kusa har takai ya hana wadanda aka gayyata amsa gayyatar hukumar shine ma dalilin da yasa tayi amfani da karfin ta, wajen kamo su.

Gwamantin Kano ta kafa kwamitin shugabanci rikon kwarya na kasuwar kantin kwari

Yanzu haka dai an cigaba da bincike domin sanin yadda ake karbar wadannan kudade.

Wakilin mu Nasiru Salisu Zango ya rawaito mana cewa, wani babban dan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa yace, tuni yasa lauyansa ya rubutawa takardar korafi kan yadda aka kama wani bakonsa dan kasar waje akan zaunar dashi a ofis kan lallai sai ya biya Naira miliyan guda.

To amma a cikin hirar mu dashi manajan darektan kasuwar ta kwari wanda har yanzu ba a fitar da jadawalin dokar tafiyar da ofis din sa ba.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/01/KWARI.mp3?_=1

Amma har an fara karbar kudade ciki har da tilashin naira miliyan guda ga ‘yan china sai dai yace executive pawer ce yake amfani da ita kafin dokar su ta aiki ta nuna.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!