Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamantin Kano ta kafa kwamitin shugabanci rikon kwarya na kasuwar kantin kwari

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da kafa kwamitin shugabancin rikon kwarya na kasuwar Kantin Kwari dake nan Kano da zai jagoranci kasuwar na tsohon shekaru uku anan gaba.

Sabon kwamitin zai tabbatar da an samar da jagoranci na gaskiya kasuwar, tsaro da tsafta tare kuma da karbar hakkokin gwamnati da suka shafi haraji da dai sauran su.

Haka zalika, kwamitin zai hada hannu da ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta jihar Kano domin shirya zabe sabbin shugabannin zartarwar kungiyar ‘yan kasuwar nan ba da dadewa ba.

Cikin shugabannin da ka nada akwai: Hajiya Rabi Mansur Yola ta Ma’aikatar kasuwanci a matsayin manajan darakta ta kasuwar, sai kuma Rabi’u Mohammad Diyam na hukumar tattara haraji ta jihar Kano a matsayin daraktan kudi, sai kuma Umar Ladio a matsayin sakataren kasuwar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!