Siyasa
APC zata yi bincike kan zargin da akewa shugaban ta na kasa
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa ya kafa kwamitin ladaftarwa mai kunshe da mutum biyar wanda zai bincike zarge-zargen da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da jihohin arewa Sanata Lawan Shu’aibu, ya yi ga shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshimhole.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Lanre Isa-Onilu.
Sanarwar ta ce, kwamitin ladaftawar mai kunshe da mutum biyar zai bincika ya gani ko akwai kanshin gaskiya cikin zargin da Sanata Lawan Shuaibu ya yi na cewa shugaban jam’iyyar Adams Oshimhole, ba ya biyayya ga matakai da kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya amince da shi.
A jiya Alhamis ne dai kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa, ya kada kuri’ar amincewa da shugabanci Adams Oshimhole a yayin taron da ya gudanar karo na talatin da takwas